A wannan shekara mutane dubu dari biyu da dubu takwas da dari shida da goma sha shida ne matsalar ambaliayr ruwa ta shafa, yayin da mutane arba’in da biyar suka rasa rayukansu.
Yankunan yamma maso kudancin kasar ne ambaliyar tafi shafa a bana, inda gidaje dubu 17 da 389 suka rushe, an kuma dabbobi dubu 34 da 429 da suka mutu, abin da ya sa kungiyoyin fararen hulla da na kare hakkin dan adam da dama a kasar ke yin kira ga gwamnati da ta agazawa wadanda wannan lamarin ya rutsa da su.
Suleymane Saadu na kungiyoyin kare hakkin dan Adama a birni Konni, yace gwamnati ta yi kokari ta fitar da kididdiga a kan a barnar da ambaliyar ta yi kuma yasan gwamnati zata kawowa jama’a dauki amma kuma ya yi kira ga jama’a su kara hakuri sub a gwamnati lokaci.
A yankin Agadez, hukumomin sun tallafawa wadanda ambaliyar ruwan sama ta rutsa da su da matsunai da abinci da magani. A wannan yanki kuma ambaliyar ta rushe gidaje, lalata filayen nomar abinci kana ta hallaka dabbobi da dama.
Magajin garin Dabaga daya daga cikin wuraren da ambaliayr ruwa ta bana ta taba, ya yi0 kira ga hukumomi da kungiyoyi na cikin gida da na wajje da abokanan huldar gwamnati da su kallesu da idanuwan rahama, su kawo musu dauki.
Haruna Mamane Bako ya aikowa Sashen Hausa na Muryar Amurka rahoto a kan haka:
Facebook Forum