Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Barrack Obama A Wurin Babban Taron Democrats Na Kasa


Foto Achiv: Ansyen Prezidan Etazini Barack Obama.
Foto Achiv: Ansyen Prezidan Etazini Barack Obama.

Barack Obama ya gabatar da jawabi mai karfafa zuciya da kyakyawar fata akan takarar mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris.

Ya ce, ina da kyakyawar fata domin tarihi ya nuna cewa wannan taron yana zama alkhairi ga masu irin sunan nan wadanda suke da Imani a kasar da komai yana iya faruwa. Bisa dalilin cewa muna da damar mu zabi mutumin da kusan tsawon rayuwar ta take kokarin ganin cewa ta baiwa mutane irin damar da Amurka ta ba ta. Wace ta san halin da kuke ciki, wacce zata saurare ku, sannan wacce zata tashi a kullum don ta yi aiki a domin kai. Ba kowa nake nufi ba illa shugaban kasar Amurka na gaba, Kamala Harris.

Shekaru 16 kenan yau, bayan da na amince da tsaida ni a matsayin dan takarar jam’iyyar Democrats, sbun Kaman jiya ne don babu abun da ya sauya a jiki na amma haka yake. Idan nayi waiwaye, babu tantama babban matakin da kuka dauka na ayyana ni a matsayin dan takarar jam’iyyar Democrats a wannan lokacin, shi ne ya zama mafi mahimanci a rayuwa ta, bayan nan sai na bukaci Biden yayi aiki da ni a matsayin mataimaki na. Kuma banda cewa yana da jinin turawan Ireland, mun zama tamkar ‘yan uwa. Yayin da mukayi aiki tare tsawon shekaru 8 masu wuya, na fahimci wani abu mai ban saha’awa akan Joe Biden; baya ga fikirar shi da gogewar shi, tausayin shi da kyakyawar halin shi wanda ya bashi karfin hali da imanin cewa kowa a kasar nan na bukatar a bashi dama. Kuma a shekaru 4 da suka gabata, Amurka ta kasance cikin bukatar wadannan dabi’u.

Barrack Obama ya tabo batutuwa da dama a cikin jawabin nasa sannan ya caccaki tsohon shugaban Amurka Donald Trump. Ya kuma yi kira ga al'ummar Amurka baki daya da su yi kokari su fahimci juna, la'akari da cewa rarrabuwan kawuna ne yana mummunan tasiri tsakani al'ummar kasar.

Itama uwar gidar sa Michelle Obama wace ta gabatar da jawabin ta gabanin Obama ta tabo mahimman batutuwa inda ta fara jawaban ta da jan hankalin 'yan kasa akan mahimmancin jajircewar da magabatan su sukayi don basu rayuwa mai ma'ana. Ta ce iyayensu basu yadda da masu handama ba, tace iyayen su sun yi imani da taimakawa 'yayan wasu don ko da su basu samu damar more amfanin su ba, 'yayan su ko jikokin su zasu ci gajiyar sadaukarwar da sukayi, sun kasance masu kyakyawar fata.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG