Da alama makwafciyar Najeriya wato Kamaru tana samun nasara akan 'yan kungiyar Boko Haram.
Kamar yadda rahoton da wakilin Muryar Amurka ya aiko daga Kamaru yace ranar Juma'a da ta gabata mayakan Boko Haram dari shida suka tsallaka tafkin Chadi daga Borno suka shiga kasar. Bai daya suka kai hare-hare akan wasu kauyuka da birane.
A fafatawar da suka yi da sojojin Kamaru, jami'ai sun ce an kama 'yan Boko Haram 25 kuma daruruwansu ruwa ya cinyesu a cikin tafkin. Ministan watsa labaru na kasar Kamaru Isa Chiroma Bakari yace an yi mummunar fafatawa a wasu kauyuka guda biyar a lokacin da sojojin gwamnati suka yi kokarin kwato kauyukan daga hannun 'yan tawayen.
Bakari yace daruruwan wadanda ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kusa cikin Kamaru daga tafkin Chadi wanda ya hada iyaka da Najeriya da Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Nijar. Ana kautata zaton 'yan yakin sun fito ne daga Maiduguri dake arewacin Najeriya.
An bada rahoton cewa sun yi barna a wasu kauyukan kasar Kamaru har da sace dabbobi da kaji. Bakari yace da karfin tsiya su ma sojojin Kamaru suka mayarda martani suka fatattaki 'yan tawayen suka tilasta masu janyewa.
Rundunar sojojin Kamaru ta kama mahara 25 tare da kashe wasu da damansu. Haka kuma daruruwansu ruwa ya cinyesu a tafkin Chadi lokacin da kwale-kwalensu suka nitse yayin da suke kokarin arcewa.
Yayin da ake fafatawa a kauyuka sai wasu 'yan kungiyar suka kai hari a kan garuruwa uku. Mai magana da yawun sojojin Kamaru yace sun kwace makamai tare da kone motoci ashirin na 'yan tawayen ciki har da tankin yaki. Yace 'yan tawayen sun yi anfani da manyan makamai suna tsammanin idan suka kara kaimin hare-harensu zasu kasara iyawar kasar Kamaru na fatattakarsu ko kuma tunkararsu.
Sojojin Kamaru ashirin ne suka ji rauni kuma an kaisu babban asibitin Marwa a arewacin kasar yayin da aka kai 'yan Boko Haram 25 da aka cafke wani wuri da ba'a bayyana ba. Babu sojan Kamaru daya da ya rasa ransa.
Ga karin bayani.