Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rigingimun Boko Haram Sun Hallaka Malaman Makaranta 250 a Arewa Maso Gabas


Maharba da suke taimakawa wurin yakar 'yan kungiyar Boko Haram a Borno.
Maharba da suke taimakawa wurin yakar 'yan kungiyar Boko Haram a Borno.

Kimanin malaman firamare da na fiye da firamare 250 suka gamu da ajalinsu sakamakon rigingimun da aka sha fama dasu da kungiyar Boko Haram cikin shekaru uku da suka gabata.

Shugaban kungiyar malaman makarantun firamare na jihar Borno Kwamred Bulama ya shaidawa Muryar Amurka lokacin da kungiyar ke raba kayan tallafi wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Malaman sun rasa rayukansu ne sakamakon rigingimu 'yanbindiga da fashewar bama bamai da suka addabi jihar Borno. Bulama yace matakin da suka dauka ya zama dole ganin cewa sun tallafawa iyalan wadanda suka rasa mazajensu, 'yanuwansu da iyalansu wadanda suka gamu da ajalinsu a hannun 'yan Boko Haram.

Tallafawar nuni ne cewa basu manta da 'yanuwansu ba wadanda suka sadakar da rayukansu domin koyawa 'ya'yan jihar ilimi. 'Ya'yan kungiyar dake duk fadin jihohin arewa maso gabas, wato Adamawa, Yobe, Taraba, Bauchi, Gombe da Borno din suka yi karo-karon nera miliyan daya suka sayi kayan da aka raba. Ban da kayan sun raba kudi nera dubu goma goma ga kowane iyali.

Kawo yanzu malamai dari biyu da hamsin suka rasa rayukansu. An rabawa iyalan malamai hamsin kuma za'a cigaba da yin hakan har sai an rabawa duk sauran iyalan.

Wadanda suka ci gajiyar kayan da aka raba sun yiwa Allah godiya da kungiyar malaman da ta shirya tallafin.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG