Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bama-bamai da Suka Fashe a Jos Sun Hallaka Akalla Mutane 16


Wani da harin bam ya rutsa dashi a Jos jihar Filato
Wani da harin bam ya rutsa dashi a Jos jihar Filato

Rundunar tsaro ta Jos jihar Filato ta tabbatar da tashin bama-bamai da kuma asarar rayuka.

Bama-baman sun fashe ne a kasuwar Terminus dake tsakiyar birnin Jos.

Kakakin rundunar tsaron jihar Filato Keften Ikedichi Iweha yace sun tantance adadin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka jikata. Yace an rasa mutane 16 kana 25 kuma suka samu raunuka.

Rundunar 'yansandan ta gargadi mutane su lura tare da bada rahoto akan duk wanda basu yadda dashi ba kafin a sake aikata wata ta'asar.

Jami'in hukumar dake bada agajin gaggawa mai kula da arewa ta tsakiya Abdulsalam Muhammad yace sun yi nasarar kwashe wadanda suka rasu da wadanda suka samu raunuka zuwa asibitoci.

Wadanda abun ya faru a idanunsu sun ce sun taso daga kasuwa ne sai kawai suka ji fashewar bam na farko. Kafin su yi nisa sai na biyu ya fashe.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG