Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya da Maharba da 'yan Kato da Gora sun Doshi Michika


Wata tankar sojan Najeriya tana sintiri a cikin garin Mubi Jihar Adamawa bayan da aka kwace garin daga hannun 'yan Boko Haram.
Wata tankar sojan Najeriya tana sintiri a cikin garin Mubi Jihar Adamawa bayan da aka kwace garin daga hannun 'yan Boko Haram.

Jama’ar, garuruwa Mubi da Maiha na bukatar tallafin Gwamnatin jihar Adamawa.

Dakarun sojojin Najeriya, da Maharba, da kuma 'yan Kato da gora,wato Civillian JTF, sun doshi, garin Michika, wanda ke cikin yakunnan, da 'yan Boko Haram, ke rike dashi.

Jama’ar, garuruwa Mubi da Maiha sun yi kira ga Gwamnatin jihar Adamawa, da ta taimaka masu da magunguna da kayayyakin kiwon Lafiya da kuma bude asibitocin dake kulle domin agazawa wadanda ke fama da rashin lafiya.

Sun kuma bukaci da a dawo masu da layuka na sadarwa, domin tuntubar juna, Suka ce maido da layuyuka zai taimaka wajen gudanar da harkokin kasuwancin su da kuma na yauda kullum.

Jama’a, har ila yau sun bukaci Karin jami’an, tsaro domin karawa jama’a karfin gwiwar dawowa garuruwan nasu.

Sakataren hukumar kai dauki na jihar Adamawa Alhaji Haruna Hammanfuro, yace hukumar zata kai wa jama’ar, dake bukatar taimako dauki batare da jikiri ba.

Sojojin Najeriya da Maharba da 'yan Kato da Gora sun Doshi Michika - 2'41"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG