KADUNA, NIGERIA - Da daren Talatar da ta wuce ne 'yan-bindigan su ka afka wa garin Yakawada da ke karamar hukumar Giwa inda su ka sace mutane tara sannan su ka harbi mutane uku har daya daga ciki ya rasu, a cewar daya daga cikin al'ummar yankin.
Kafin sace mutanen dai an ce 'yan sa kai sun yi kokarin dakile harin, sai dai ba su yi nasarar hakan ba, inji daya daga cikin 'yan sakan da aka yi artabu da su.
Mun yi ta kiran wayar shugaban karamar hukumar ta Giwa game da wannan hari, to sai dai wayar shi ta na kashe kuma mun tura sakonni amma bamu samu amsa ba har zuwa lokachin hada wannan rahoton. Ko da ya ke dai gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasuru Ahmed El-rufa'i, ya sha nanata bukatar dauki daga gwamnatin tarayya game da wannan matsala ta tsaro.
Kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari, da Igabi dai na cikin kananan hukumomin da ke shiyyar Kaduna ta tsakiya da ke fama da hare-haren 'yan-bindiga da sauran matsalolin tsaro baya da wasu yankunan kudancin Kaduna.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara: