WASHINGTON, D.C - Jinkirin sakin sama da mutane 60 da 'yan-bindiga su ka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna dai ya sa dole 'yan'uwan wadanda aka sacen kai-komon ganin 'yan'uwan su su kubuta abun da ya sa 'yan-bindigan ke ta sakin fasinjojin jirgin kasan kashi-kashi kuma wadanda aka sako yau Laraba duka 'yan gida daya, banda wata dattijuwa 'yar shekara 60 da aka ce ciwo ne ya yi tsanani aka saka ta cikin wadanda aka sako.
Shugaban kamfanin jaridar Desert Herald, Malam Tukur Mamu ya ce a ma daina boye-boye akan amfani da kudi wajen ceto wadanda ke dajin.
Malam Abubakar Idris Garba mai-dakin matar da aka sako kuma mahaifin yaranta da aka sako a wannan Laraba ya ce ya na da roko ga gwamnatin tarayya.
Har yanzu dai fasinjojin jirgin kasan 27 na daji kuma mahafiya da ya’yan Abdul-Azeez Attah na cikin wadanda ba a sako ba saboda haka ya ce su na cikin damuwa.
Wasu 'yan'uwan da ba a sako na su ‘yanuwan ba sun shedawa Muryar Amurka cewa kudi ake bukata wanda ba su da shi amma su nan su na ta karo-karo.
Saurari cikakken rahoton daga Isah Lawal Ikara: