'Yan bindiga sun kashe mutane biyu kuma sun yi garkuwa da mutane sama da talatin da biyu, sannan sun karbe mulkin kauyukan Jauro Manu da garin Gidado da kuma yankin Jauro Aji da ke Karamar Hukumar Gassol A jihar taraba.
'Yan bindigar sun kuma tare babbar hanya da kuma mototin da suke dauko mutane zuwa kasuwan kauye saku kashe direban su ka yi awongaba da fasinjoji masu tafiya cin kasuwan kauyen.
Wani da lamarin ya faru a idonsa kuma mazaunin yankin Jauro Manu, ya ce yanzu haka mutanen da su ka tsere suna gudun hijira a garin Mutum Biyu da ke Karamar Hukumar Gassol A jihar Taraba
Ya ce kauyukansu ba kowa sai 'yan bindiga, kuma su ke mulki a yankin; sai kuma wandanda 'yan bindiga suka hana su gudu ko kuma basu sami sararin gudun ba.
Yahaya Ma'azu Abubakar mazaunin garin Garba Chede da ke Karamar Hukumar Bali ya bukaci da mahukuntan a Nigeria su kawo musu daukin gaggawa domin rayuwarsu na chikin hadari
Dan Majalisa mai wakiltar Bali da Gossol a Majalisan Wakilan na taraiyyar Nigeria, Abdullasalam Gambon Mubarak ya tabbatar da hakan a hirar da Sashin Hausa ya yi da shi ya tabbatar da cewa yanzu haka suna tattaunawa da jami'an tsaron Nigeria don kawo karshen 'yan ta'addar da suka kwace yankunan gaba daya.
Saurari cikakken rahoton Mohammed Salisu Lado: