Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Halaka 'Yan Sanda A Kogi Da Imo


'Yan Bindiga Sanye Da Kakin Soja
'Yan Bindiga Sanye Da Kakin Soja

Jami'an 'yan sanda hudu a jihar Imo da kuma wasu biyu a jihar Kogi sun gamu da ajalinsu yayin wasu hare-haren ‘yan bidiga a jihohin biyu a ranar Juma'a.

‘Yan bidiga da ba a tabbatar da ko su wanene ba sun halaka ‘yan sanda hudu yayin wani mummunan hari kan babban ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Oguta a jihar Imo dake kudancin kasar.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, Mike Abattam wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce a daren Juma’a ne ‘yan bindigar suka danna ofishin ‘yan sandan, inda suka koma motoci da wani bangare na ofishin.

Kwamishinan ‘yan sand ana jihar Imo, Mohammed Barde ya ziyarci wurin da abin ya faru don tantance munin harin.

Barde ya bukaci mutane a yankin da su kwantar da hankalinsu, ya na mai tabbatar mu su cewa rundunar ‘yan sanda za ta magance matsalar.

Kai hari kan ofishin ‘yan sanda ba sabon abu ba ne a jihar Imo, domin ko a watan Afrilu, rahotanni sun nuna an kai hare-hare a ofisoshin ‘yan sanda akalla biyar a fadin jihar

Wasu daga cikin hare-haren, an dora alhakinsu ne akan kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra, wato IPOB.

'Yan Bindiga Na Ci Gaba Da Addabar Sassan Najeriya Daban Daban
'Yan Bindiga Na Ci Gaba Da Addabar Sassan Najeriya Daban Daban

A wani labarin kuma, rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun halaka akalla jami’an ‘yan sanda biyu a jihar Kogi dake arewa ta tsakiya a Najeriyar, yayin wani hari a karamar hukumar Ajaokuta.

Rahotannin sun ce ‘yan bindigan sun sace wasu mutane goma sha hudu da ake tunanin ‘yan kasar Indiya ne a lokacin harin ranar Juma’a.

Gwamnatin jihar Kogi ta ce ta na daukan matakan da suka dace domin ganin an kubutar da mutanen goma sha hudu.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce an kara daukan tsauraran matakan tsaro a duk fadin jihar, yayin da ake ci gaba da samun hare-hare.

‘Yan bindiga dai na ci gaba da kar hare-hare musanman a arewacin Najeriya, wanda ke halaka mutane da dama da kuma tilastawa wasu gudun hijira.

XS
SM
MD
LG