Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mata Bakwai Da Jarirai Biyu A Katsina


FILE PHOTO: 'Yan Bindiga
FILE PHOTO: 'Yan Bindiga

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wata Majami’a a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, tare da yin garkuwa da mata ciki har da masu shayarwa da jarirai.

Da safiyar ranar Lahadi ne baraya daji dauke da makamai ciki har da bindigogi kirar AK-47 da ba a tantance yawansu ba, sun afkawa Majami’ar New Life Church dake kauyen Dan Mai Tsauni, dake karamar hukumar Kankara.

Da yake tabbatarwa da Muryar Amurka faruwar lamarin Kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce lokacin da yan bindigar suka isa Majami’ar sun afkawa limamin Cocin da duka har suka karya masa hannu.

Yanzu haka dai ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mata bakwai da kananan yara zuwa cikin daji, sai dai jami’an tsaro sun tabbatar da datse dukkan hanyoyi domin ci gaba da kokarin ganin an ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Yankin karamar hukumar Kankara na jihar Katsina na daga cikin wuraren dake fama da matsalar tsaro a arewacin kasar. Tun farko ana zargin fatattakar yan bindigar da ake yi daga wasu wurare da suka hada da yankunan jihar Zamfara, na daga cikin dalilan da suka kara ta’azzara lamarin tsaro.

Domin karin bayani saurari rahotan Sani Shu’aibu Malumfashi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG