Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Dan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Jim Kadan Bayan Bikin Komawa APC


Marigayi Muhammad Ahmad, Dan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara.
Marigayi Muhammad Ahmad, Dan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara.

Honarabul Muhammad Ahmad na daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar na jam’iyyar PDP da suka bi gwamna Matawalle a sauya sheka zuwa APC.

‘Yan bindiga sun harbe dan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar mazabar Shinkafi.

Dan majalisar ya gamu da ajalinsa ne akan hanyarsa ta zuwa Kano, jim kadan bayan kammala bikin karbar gwamnan jihar ta Zamfara zuwa jam’iyyar APC a ranar Talata.

Honarabul Muhammad Ahmad na daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar na jam’iyyar PDP da suka bi gwamna Matawalle a sauya sheka zuwa APC.

Rahotanni sun bayyana cewa dan majalisar na kan hanyarsa ne ta zuwa Kano domin ajiye dansa da zai yi tafiya a filin jirgin sama, to amma kuma dan na shi da ma direbansa duk sun kubuta ba tare da jin wani rauni ba.

Karin bayani akan: APC, PDP, Kano, 'Yan Bindiga​, Majalisar Dokokin​, gwamnan, jihar Zamfara, Bello Matawalle, Muhammad Ahmad, Nigeria, da Najeriya.

Ahmad malamin makaranta ne kuma dan kasuwa kafin ya shiga harkokin siyasa.

Kafin rasuwarsa, shi ne shugaban kwamitin majalisar dokoki kan sha’anin kudi da kasafin kudi.

Wata sanarwa da babban daraktan watsa labarai na majalisar dokokin jihar Zamfara ya fitar, ta ce an yi jana’izar marigayin da safiyar Laraba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG