Kungiyar daliban jami’o’in Najeriya NANS, ta kai wa Sheikh Ahmad Gumi ziyara a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.
Wata sanarwa da shugaban kungiyar Sunday Asefon ya wallafa a ranar Litinin ta ce, tawagar daliban ta tattauna da Shehin malamin kan al’amuran da suka shafi kare lafiyar daliban Najeriya a duk jami’o’i da kuma matakan da za a bi don sako wadanda aka yi garkuwa da su.
“Mun yi magana kan yadda za a ci gaba da tattaunawa dangane da yadda za a sako daliban da aka sace da kuma matakan da ya kamata a bi wajen ganin an tabbatar da cewa makarantu suna da cikakken tsaro.
Karin bayani akan: Zaria, jihar Neja, Sheikh Ahmad Gumi, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
“Saboda dalibanmu su gujewa fargabar yiwuwar a yi garkuwa da su.” Asefon ya ce.
“Za mu ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don tabbatar da tsaro a makarantu.” Shugaban na NANS ya ce.
A ‘yan watannin baya Sheikh Ahmad Gumi, ya kan shiga daji don ya yi wa 'yan fashin dajin wa'azi tare da sauraren korafe-korafensu.
A baya-bayan nan ‘yan bindigar sun sace dalibai da malamai a kwajelin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke garin Zaria.
Kazalika sun sace dalibai sama da 100 a wata makarantar Islamiyya da ke garin Tegina a jihar Neja.
Sannan sun yi garkuwa da daliban sakandaren gwamnatin tarayya da ke Yawuri a jihar Zamfara.
Har yanzu ba a jin duriyar dukkan wadannan dalibai da aka sace.
‘Yan bindigar kan nemi a biya su miliyoyin kudade kafin su saki mutanen da suka yi garkuwa da su a Najeriya.
Hukumomi a matakin jiha da tarayya sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun magance matsalar tsaron musamman wacce ta shafi satar mutane don neman kudin fansa.