Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, rasu zanga-zangar fito ne a kauyuka daban-daban da ke kan titin na Gusau zuwa Kaura Namoda a safiyar yau Litinin, inda suka sanya shingaye tar da hana kowa wucewa akan titin, lamarin da kuma ya juye zuwa tarzoma a wasu wurare.
Matasan na nuna fushinsu ne akan abin da suka ce "tura ta kai bango a yawan hare-hare da ‘yan bindiga ke kaiwa a kowace rana ta Allah a garurruwansu.
An jiyo masu zanga-zangar na cewa a kullum ba sa samun kwantawa bacci, saboda zaman dar-dar da fargabar garin da yan bindigan za su iya afkawa, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Wani matafiyi wanda ya tsinci kan sa cikin cunkoson ababen hawa kan titin na Gusa zuwa Kaura Namoda ya bayyana cewa, matasan sun rufe babbar hanyar dake kan mahadar yankin Kurya inda suka fara lalata motocin jama'a da ke tafiya a kan hanyar.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa masu zanga-zangar da suka hada har da 'yan sa kai, wadanda wasunsu ke rike da makamai, ciki har da bindigogin gargajiya, sun kai farmaki kan wata tawagar jami'an 'yan sanda da suka yi kokarin zuwa domin kwantar da tarzomar.
Fusatattun matasan dai sun yi Allah wadai da hare-haren yau-da-kullum da yan bindiga ke kaiwa wanda ya ki ci ya ki cinyewa a garurruwan su, lamarin da su ka ce ya ke neman ya gaggari gwamnatin tarayya inda suka bukaci gwamnati ta samo mafita mai dorewa saboda "tura ta kai bango."
Kawo zuwa lokacin hada wannan rahoto, duk kokarin ji ta bakin rundunar yan sandan jihar Zamfara kan wannan zanga-zanga ya ci tura.
Hare-haren 'yan bindiga dai ya kara uzzura a jihar ta Zamfara a baya-bayan nan, bayan kasawar shirin sulhu da gwamnatin jihar ta soma yi da 'yan bindigar.
A makon jiya ma sai da mazaunan garin Gauraka da ke karamar hukumar Tafa na jihar Neja suka rufe titin Abuja zuwa Kaduna a wani mataki na bayyana bacin ransu ta hanyar yin zanga-zanga don neman gwamnati ta kawo karshen matsalolin masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da ayyyukan ‘yan bindiga a jihar da ma kasa baki daya.
Idan ana iya tunawa kuma, wasu kungiyoyin fararren hula sun yi zanga-zangar tura ta kai bango zuwa harabar majalisun kasar a makon na jiya, don neman gwamnati ta dauki matakan gaggawa kafin al’umma su fara daukar mataki a hasnun su.