Dan kunar bakin waken, wanda yace sunanshi ‘Abubakar’, a halin yanzu yana hannun jami’an tsaro, kuma tuni an kwance kayan bom din da yake dauke da su.
Jihar Yobe na daya daga cikin Jihohin arewa maso gabashin Najeriya dake fama da rigigimu, inda ‘yan kungiyar da aka fi sani da Boko Haram suke kone-konen gidaje, da kisan kan mai uwa da wabi. A makwabciyarta Borno, misalin makonni uku kennan da sace dalibai mata sama da 200 ‘yan makarantar Sakandare dake Cibok, wadanda har yanzu ba’a san halin da suke ciki ba.
Gwamnan daya daga cikin Jihohi uku wato Borno Yobe da Adamawa da suka share kusan shekara daya karkarshin dokar-ta-baci, Murtala Nyako na Adamawa, ya zargi shugaba Jonathan da hannu a tashe-tashen hankula da ake fama da su a arewacin Najeriya, inda yayi alwashin tattara takardun shaida domin kai kara a kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa dake birnin Hague. Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin Admiral Murtala Nyako mai ritaya.