Daya daga cikin iyayen yaran wadda bata so a fadi sunnanta tace ”ta fuskar gwamnati ma muyi kuka munyi magana har a Muryar Amurka ma munyi magana a matsayin iyaye, muna neman gwamnati ta taimake mu har rana mai kama ta yau bamu ji komai akai ba.”
Ta kara da cewa “mu bakin cikin mu shine, mu da yaranmu suka bata, mun fisu bakin ciki duk wanda aka ce dansa ya bata gara ya ga gawarsa ya tabbatar yayi imani ga Allah cewa wannan dan fa rasuwa yayi, da ace maka danka ya bace har yau ba abunda aka ce mana, ba wani taimako da aka yi mana, kuma ‘ya'yan mu amana muka dauka muka sa a hannu su amma da abu ya faru sai aka barmu mu kadai muke ta bin kauyuka.”
Tayi kuma kira ga gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima da don Allah yasa a duba domin suna sa ran cewa suma tafiya dasu akayi.
Wakilin Muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari, yayi kokarin jin ta bakin gwamnatin jihar Yobe domin jin nasu bangaren amma hakan bai samu ba, domin ya kira lambar kakakin gwamnar jihar Yobe Abdullahi Bego, bata samu ba, yayin da wasu ke tunanin cewa yaran sunna hannun masu tada kayar baya.