Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Boko Haram Sun Kai Hari Wani Asibiti A Arewa Mai Nisa


Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari a asibitin Mada da ke yankin Arewa mai Nisa a kasar Kamaru cikin daren Juma’a zuwa Asabar.

A cewar majiyoyin tsaro, an kashe wani mai gadi a wannan asibitin tare da jikkata wasu ma’aitakata da kuma marasa lafiya da dama masu jinya a wannan asibiti.

Boubakari Ahmadou daya daga cikin wadannan suka tsira daga wannan aika aika ya shaidawa muryar Amurka cewa “Mayakan Boko haram sun iso cikin dare tun daga kofa suka soma harba bindiga. Muna daga ciki mu ka hango yadda suke zuba man fetur a jikin gini, da mai gadi ya nemi ya tsare su sai suka kashe shi. Bayan haka suka kona asibiti. Suka kuma dauke kayan abinci da aka tara a asibiti saboda marasa lafiya. Zuwan sojojin Kamaru ne ya sa suka zabura, suka ari ta kare”.

Maharan sun kuma kona asibitin Mada kurmus. Haka zalika suka kona motocin daukan marasa lafiya da babura.

Wata kungiya mai zaman kanta Humanity Purpose ta ce, an yi garkuwa da wasu sojojin Kamaru a yayin harin, amma babu wata majiya a hukumance da ta tabbatar da wannan garkuwar.

Boubakari ya kara da cewa “A wannan yankin Mada, tun da matsalar Boko Haram ta bayyana, muna fiskantar hare hare a kowace damuna. Saboda yanayi na sanya jami’an tsaro su koma daga cikin mayan kauyuka saboda hanyar zuwa Mada bata da kyau. Da duk kokarin da hukumomin mu suke yi, dole ne jami’an tsaro su koma da baya. Muna fatar gwamnati za ta mai da hankali kan wannan yakin bayan wanan hari da Boko haram suka kai”
A 'yan watannin da suka gabata kungiyar Boko Haram ta kara kai hare-hare a yankin Arewa mai nisa inda yanayin tsaro ya yi karanci 'yan kwanakin nan.

Shugaban kasa Paul Biya ya aika da ministar da ke kula da harkokin tsaro, Joseph Beti Assomo zuwa yankin arewa mai nisa, domin farfado da sojojin, da kuma kara musu kwarin gwiwa da nufin shawo kan wannan matasala.

Saurari cikakken rahoton Mohamed Ladan cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG