Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Tashar 'Yan Sandan Petelkole A Iyakar Nijar Da Burkina Faso


Wasu motoci da 'yan bindiga suka kona.
Wasu motoci da 'yan bindiga suka kona.

Maharan sun fara ne da harba rokoki akan wasu motocin ‘yan sanda biyu kirar VAB masu dauke da manyan bindigogi kafin su bude wuta akan ‘yan sandan dake aiki a wannan tasha.

A Jamhuriyar Nijar ‘yan bindiga sun kai hari a tashar binciken ‘yan sanda ta kauyen Petelkole dake gundumar Tera ta jihar Tilabery iyaka da Burkina Faso a yammacin ranar Talata inda suka hallaka ma’aikata tare da kona wasu motoci kafin su arce da manyan makamai.

Lamarin ya faru ne da goshin Magaribar ranar 12 ga watan Afrilu inda wasu mutane masu tarin yawa dauke da bindigogi suka afkawa tashar bincike ta Petelokle a gundumar Tera jihar Tilabery kan iyakar Nijer da Burkina Faso.

Maharan sun fara ne da harba rokoki akan wasu motocin ‘yan sanda biyu kirar VAB masu dauke da manyan bindigogi kafin su bude wuta akan ‘yan sandan dake aiki a wannan tasha.

Ko da yake, kawo yanzu hukumomi ba su yi bayani a game da abubuwan da suka wakana ba a yayin wannan hari majiyoyi sun tabbatar da rasuwar ‘yan sanda hudu wasu hudu kuma sun yi batan dabo sannan 16 sun ji rauni da dama daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

Haka kuma ‘yan bindigar sun yi awon gaba da motoci 3 masu dauke da mayan bindigogin yaki.

Nadar muryoyin mazaunan wannan yanki ya faskara saboda fargabar abinda ka iya kibo baya to amma a nan Yamai.

Wani dan rajin kare hakkin jama’a na kungiyar Sauvons le Niger Salissou Amadou ya bayyana takaicinsa game da faruwar wannan al’amari a wannan lokaci na tausayawa juna.

Da ma dai tun a washegarin daukar matakin sassauta dokar hana zirga- zirgar babura a da’irar Tilabery a makon jiya sakataren kungiyar ‘yan jarida masu kula da sha’anin tsaro Ibrahim Moussa ya ja hankula akan abubuwan da ka iya biyo bayan wannan yunkuri a bisa la’akari da manufofin ‘yan ta’adda saboda haka ya sake nanata wannan kira.

A tsakiyar watan Maris din da ya gabata wasu fasijnjoji kusan 20 na motar kamfanin STM da suka fito daga Ouagadougou zuwa birnin Yamai sun hadu da ajalinsu a wani wurin dake gab da tashar bincike ta Petelkole bayan da suka fada tarkon ‘yan bindigar, lamarin da ya rutsa da wasu ‘yan sanda biyu sannan suka cinna wa motar wuta hade da wata trelar dakon kaya.

Saurari cikakken rahoton cikina sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG