Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Gomman Fasinjoji A Nijar


‘Yan bindiga sun afka wa wata motar jigila mai dauke da fasinjoji sama da 40 akan hanyarsu ta zuwa birnin Yamai bayan da suka fito daga birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, cikinsu har da ‘yan sanda uku.

NIAMEY, NIGER - Lamarin ya faru ne da rana tsaka a jiya Laraba lokacin da ‘yan bindiga suka tare wata motar jigilar kamfanin STM a wani wurin dake a tazarar km 5 da tashar binciken kan iyakar Nijar da Burkina FASO wato a tsakanin kauyen Fono da kauyen Zelangue na biyu a gundumar Tera . Rahotanni na nuni da cewa, maharan sun hallaka akasarin wadanan fasinja.

Motar kirar bas mai dauke da fasinja 43 ta fito ne daga birnin Ougadougou cikinsu har da ‘yan sanda uku da ke shirin komawa gida bayan kammala aikin mako-mako a tashar binciken iyaka.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, ‘yan bindigar sun kona motar sannan su ka karkashe mutanen dake cikinta in ban da wasu mata uku da suka tsira da ransu yayinda daya daga cikin ‘yan sandan uku ya ji mummunan rauni.

Magajin garin Tera, Hama Mamoudou ya tabbatar da faruwar wannan al’amari. Koda yake ya ce ba shi da masaniya game da zahirin adadin mutanen da suka rasu sanadiyar wannan hari.

Haka kuma maharan sun kona wata mota kirar telem wato Trela Tuni aka kwashe gawarwakin wadanan mutane aka ajiye su a dakin ajiyar gawa na asibitin Tera domin aikin tantancewa kafin a nan gaba a yi jana’izarsu ko kuma a damka su ga danginsu.

Shugaban Nijar Mohamed Bazoum Ya Shaida Mana Dalilin Da Yasa Kasarsa Ta Amince Ta Karbi Sojojin Faransa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Kamfanin jigila na STM ya tabbatar da faruwar wannan al’amari haka kuma Muryar Amurka ta yi katari ganin wata kanwar dreban da abin ya rutsa da shi ta isa a cibiyar kamfanin na STM cikin sheshekar kukan wannan rashi.

Wannan shine karon farko da ‘yan bidigar yankin Tilabery ke tare motar fasinjoji, abinda ke nunin yadda masu tada kayar baya ke kokarin karkatar da ayyukansu wajen huce takaici akan fararen hula wanda masana sha’anin tsaro ke kallonsa a matsayin wata alamar dake nunin jami’an tsaro sun ci karfin kungiyoyin ta’addancin iyakokin Mali, Nijar da Burkina Faso misalin yadda a bayan nan suka karkatar da ayyukansu wajen dasa nakiya akan hanyoyi.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Akan Wata Motar Jigila Tare Da Hallaka Gommai Daga Cikinsu
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

XS
SM
MD
LG