Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari A Gombi Dake Jihar Adamawa


Wasu 'yan sandan Nijeriya a bakin aiki
Wasu 'yan sandan Nijeriya a bakin aiki

Al Ummar karamar hukumar Gombi da kewaye, dake jihar Adamawa na yanayin zaman dar dar bayan wani dirar mikiya da wasu yan bindiga suka kai wa ofishin ‘yan sanda dake wannan gari.

Wannan hari ya kashe wasu ‘yan sanda tare da raina wasu.

Shaidun gani da ido sunce mutanen dake dauke da bindiga, sun share lokaci mai tsawo suna barin wuta.

“Wasu mutane da bindigogi suka shigo, suka kai hari a Divisional Headquarters na garin, suka yi ta harbe-harbe, sukayi boming police station din, kuma suka kona motar yan sanda a wurin, suka kashe ‘yan sanda biyu, suka raunata guda biyu”. Wadannan kalaman wani da ya ga abunda ya faru ne, kuma bai fadi sunansa ba.

Kakarin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawan, DSP Mohammed Ibrahim ya tabbatar da wannan hari.

Lamarin nan ya zone yayinda dokar Ta Baci da aka kafa a jihar Adamawan ke cika watanni hudu, kuma wannan ne karon farko da aka kai irin wannan hari, tun bayan kafa dokar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG