Hadarin tankar ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku cikinsu har da mace daya kana kimanin motoci biyar tankar ta nika. Malam Ahmed Danjida kwamandan hukumar kula da ziga-zirgar motoci da ababen hawa a jihar Gombe ya yi karin bayani inda ya ce wata tanka ce ta samu matsalar birki har ta samu ta markade irin keken nan mai kafa uku kuma guda uku da wata mota kirar honda daya. Ya ce an samu asarar rayuka biyu maza daya kuma mace.
Dangane da sakacin hukumar na rashin tabbatar da lafiyar motoci kafin su shiga hanya sai jami'in ya ce basa yin sakaci. Suna iyakacin kokarinsu. Suna hana idonsu barci su zagaya domin su tabbatar motoci na cikin lafiya kafin su kama yin zirga-zirga. Wani mataki da suka dauka shi ne hana manyan motoci kamar su tanka shigowa cikin gari. Ya ce wasu suna dakatawa har sai dare ya yi. Ya ce lokacin da babu jami'an tsaro ko kuma su basa sintiri to sai su shigo gari. Ya ce Gombe gangara ce ko ta ina ka shigo garin shi yasa suka hana manyan motocin shigowa gari. Amma duk da haka sukan shigo. Ya ce gaba daya an hana manyan motoci shigowa garin domin sun fi samun matsaloli da yawan hadura da motocin. Idan manyan motoci sun yi hadari mutane da yawa na mutuwa ba kamar kananan motoci ba. Idan manyan motoci suka rasa birki a cikin gari da wadanda suke ciki da mutanen gari kusa da hanya duk markadesu zasa yi.
Shugaban masu tuka manyan motoci ya ce hadari daga Allah ya ke domin babu direban da zai so ya yi hadari. Da aka fada masa cewa basa kula da lafiyar motocinsu kamar tabbatar da samun birki da dai wasunsu sai ya ce a matsayinsu na shugabanni suna iyakacin kokarinsu.
Abdulwahab Mohammed nada karin bayani.