Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Najeriya Sun Yi Artabu Da Maharan Da Suka Sace Daliban Kebbi


Sojojin Najeriya yayin wani atisaye da suka yi (Twitter/@HQNigerianArmy).
Sojojin Najeriya yayin wani atisaye da suka yi (Twitter/@HQNigerianArmy).

A Najeriya jama'a na kyautata zaton cewa rundunar sojin kasar na can na fafatukar ceto daliban makarantar gwamnatin tarayya dake Birnin Yauri wadanda ‘yan bindiga suka sace.

Tun a daren Alhamis rahotanni daga yankin Dirin daji da Makuku ke nuna cewa sojoji suna fafatawa da ‘yan bindiga.

Wasu rahotanni sun ce an kubutar da dalibai biyar daga cikin daliban, wadanda har yanzu ba san adadinsu ba yayin da bayanai daga hukumomin tsaro ke cewa, an kashe daya daga cikin daliban sanadiyyar musayar wuta da aka yi kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Dama dajin Makuku tuni da ya kasance hanyar da ‘yan ta'addar ke bi idan za su je ko kuma idan sun dawo daga aika-aikar su.

Amma a wannan karon sun hadu da fushin sojin Najeriya a wannan dajin na Makuku.

Wasu daga cikin daliban da suka tsira daga hain 'yan bindigar a jihar Kebbi
Wasu daga cikin daliban da suka tsira daga hain 'yan bindigar a jihar Kebbi

Mun zanta da wani mazaunin Dirin daji wanda shi ne babban garin dake kusa da dajin na Makuku, Ibrahim Dirin daji wanda ya sheda min yanayin da ake ciki game da kokari ceto daliban.

Muryar Amurka ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Kebbi, DSP Nafi'u Abubakar amma ba mu ji komai daga gare sa ba.

Karin bayani akan: jihar Kebbi, daliban, ‘yan bindiga, Abubakar Atiku Bagudu, Channels, Nigeria, da Najeriya.

A halin da ake ciki kuma gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu ya Isa garin inda aka sace daliban domin jajantawa jama'a akan lamarin.

Jama'a dai na ci gaba da addu'o'in neman samun kubutar daliban da aka kama har ma da malaman su.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Dakarun Najeriya Sun Yi Artabu Da Maharan Da Suka Sace Daliban Kebbi
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:59 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG