Rahotanni na bayyana cewa an sami wasu dalibai da ba'a tantance adadinsu ba da suka sami kubuta, daga cikin daliban makarantar gwamnatin tarayya ta Yawuri da ke jihar Kebbi, da wasu 'yan bindiga suka sace, cikin har da wata yarinya 'yar shekara 12.
Mahaifinta Malam Jibo yace ya lura da jini a kafarta.
Kawo yanzu dai shugaban makarantar Mustapha Ayuba Yusuf, ya ce ba'a iya tantance yawan daliban da yan bindigar suka sace ba.
Tuni da rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta ce ta baza jami'an ta cikin daji domin su bi sawun ‘yan bindigar.
To amma yayin da Muryar Amurka ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan domin jin karin bayani, ya amsa da cewa babu.
Wasu rahotanni daga kudancin jihar ta Kebbi kuma sun bayyana cewa sojoji sun yi ba-ta-kashi da ‘yan bindigar a yankin Dirin Daji, Makuku da Sakaba duk a cikin masarautar Zuru.
A ranar Alhamis ne dai wasu 'yan bindiga akan babura suka kai farmaki a kwalejin ta gwamnatin tarayya da ke Birnin Yawuri ta jihar Kebbi a Arewa maso yammacin Najeriya, inda suka yi awon gaba da dalibai da ba'a tantance adadinsu ba, har ma da wasu malamansu.
Wannan kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da daliban makarantar Islamiyyar Tegina da ke makwabciyar jihar Naija, suke ci gaba da kasancewa a hannun 'yan bindiga, bayan da suka sace su makwanni 3 da suka gabata.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: