Maharan sun kai harin ne kan wasu manoma da yammacin ranar litinin a kauyen Goska lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar manoman biyar tare da jikatta wani mutum.
Wasu shaidun gani da ido da ba su bayyana sunan su ba daga kauyen da lamarin ya auku sun bayyana cewa maharan sun afka musu ne da muggan makamai da suka hada da wukake, adduna, da ma bindigogi a yayin da suke tsaka da aiki a cikin gonar su.
Sun kara da cewa lamarin nan take ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu, a yayin da a ka garzaya da mutum na biyar zuwa asibiti kuma ya cika a kan gadon na asibiti da ya ke jinya daga bisani.
Rahotanni daga kauyen Gwoska sun yi nuni da cewa, tuni aka kwashe gawarwakin mutane hudun da suka rasa rayukan su tare da garzaya da mutane biyun da suka jikkata zuwa babban asibitin garin Kafanchan daga bisani.
A yayin hada wannan labarin, duk kokarin ji ta bakin kakakin rundunar ’yan sanda ta jihar Kaduna wato ASP Muhammed Jalige, ya ci tura.
Rikice-rikice tsakanin manoma da ‘yan bindiga da ke addabar su abu ne da ke neman ya gaggari gwamnati musamman a baya-bayan nan da al’ummar yankunan kudancin Kaduna karkashin inuwar kungiyar SOKAPU suka nemi ballewa daga jihar ta Kaduna a ba su ta su jihar a daidai lokacin da ake nazari kan sake fasalta kundin tsarin mulkin kasar na 1991 da ke kan gaba a halin yanzu.