Akan iyakar Najeriya da Nijar ne a birnin Konnin Jamhuriyar Nijar dake da tazarar kilomita biyar kacal da garin farko dake cikin tarayyar Najeriya aka kone duk miyagun kwayoyi da duk abubuwan dake sa ta'ammali da aka kama.
Miyagun kwayoyin ana shigowa dasu ne daga tarayyar Najeriya zuwa kasar Nijar kana su sallaka zuwa kasashen Larabawa da Turai da ma Amurka.
Malam Hamisu Shuda kwamishanan rundunar tsaro ta 'yansandan birnin Konni ya yiwa manema labarai karin bayani. Yace abun da ya faru alama ce da ta nuna irin yakin da jami'an tsaro su keyi da miyagun kwayoyi. Injish zasu cigaba da yin yakin.
Dimbin kwayar da ta kai miliyoyin sefa an konata ne a gaban alkalai da mahukuntan bariki da na gargajiya da shugabannin jami'an tsaro.
Kwamishanan 'yansandan Konni ya yiwa jam'an tsaro godiya da irin jan aikin da suka yi tare da sarakunan gargajiya da sauran al'umma dake basu goyon baya wajen yaki da miyagun kwayoyi.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.
Facebook Forum