Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Afirka Sun Sami Ci Gaba a Fannin Yanar Gizo


Dalibai a cikin aji a birnin Cape town.
Dalibai a cikin aji a birnin Cape town.

Ana kallo ko kiran abunda yake faruwa “Demokuradiyya ta internet”, wadda ya bada sabbin hanyoyin sa ido kan gwamnati da ma’aikatanta.

A fadin Afirka shafukan intenet da wasu fasahohi a woyar selula suna baiwa ‘yan kasa damar kara shiga cikin harkokin gwamnati, kama daga yin korafi idan gwamnati ta gaza a ayyukan more rayuwa, da kuma fallasa cin hanci da rashawa.

Yanzu ana iya cewa kasashen Africa sunci gaba a fannin harkokin yanar gizo, kama daga saye-da sayarwa ta anfani da duniyar gizo, musammam wurin sayen abinci ko kuma biyan kudin tasi. Ba shakka wannan canjin tsarin rayuwa ko juyin juyan halin afani da yanar gizo na kankama inji Maria Sarungi ‘yar asalin kasar Tanzania.

Sarungi dai it ace ta kirkiro da dandalin nan da ake kira CANJI A KASAR TA Tanzania, abinda farko ya fara kamar hanyar sadarwa ta zamani, amma yau ya riikide ya koma wani kasaitaccen hanyar dandalin sadarwa dake cike da da tsarin aikewa da sakonni iri daban-daban kai har ma da bukatar samar da na’urorin tsaro a wuraren tsayawar bas-bas, ko kuma bayar da yekuwar bukatar a tsabtace bakin teku na al’umma.

‘’A wani zamani nada can, mutane suna zama ne kawai a bakin titi suna maganganu game da harkokin siyasa amma yau lamarin ya sake kamannin domin wannan mutanen yau sune keda tasiri a harkan siyasa. Hakan ya faru ne sabo da anfani da hanyoyin sadarwa na zamani inda za a iya jin muryan mutun fiye da yadda ake ji ada.

Musali a kasar Uganda shafi ko kum dandalin nan da ake kira YOGERA ko kuma yi Magana, ya baiwa ‘yan kasar damar fadin albarkacin bakin su ta yadda zasu iya kai kukan su ga gwamnati ko kuma kwarmata masu wa gwamnati kuruciyyar bera

Haka shima shafin nan nan Mzalendo na kasar Kenya wanda ya mayar da kansa a matsayin idanun dake kula da al’amurrar majilisar dokokin kasar yana taka wa ‘yan siyasa birki, tare da binciken kudaden da ake kashewa na gwamnati tare kuma da bayyana yancin dan kasa.

Sai dai Sarungi tace wani hanzari ba gudu ba wannan sabon yanayi na sadarwa yana da hadarin a hannun ‘yan siyasa.

‘’Muna ganin yadda gwamnati na iya bakin kokarin ta domin ganin ta rage tasirin wannan hanyar sadarwan’’

A cikin shekarar data gabata Maxence Melo wanda shine ya sanmar da shafin kwarmaton masu satar kudin gwamnati mai suna dandalin jamil, ya fada hannun hukumar kasar Tanzania akan tuhumar sa da aikata ba dai-dai ba game da duniyar gizo domin ya gaza bata hujjar wani bayanin da akasa a wannan shafin

Jim kadan da kammala sauraren zaman bada beli, Melo yace shi da magoya bayan sa suka ce ba wai suna nuna kiyayyar su ga gwamnati bane ko kuma alkalin ko kuma rundunar ‘yan sanda, a’a amma abinda suke adawa dashi shine dokar nan ta yaki da aikata ayyukan assha ta duniyar gizo, wanda ke neman take wa mutane hakkin su

Yanzu dai a cikin watan gobe ne za a sake komawa kotu domin sauraren karar ta Melo.

A wuri daya kuma a jamhuriyar Kamaru gwamnatin kasar ta tsinke wayar sadarwa na duniyar gizo ga miliyoyin yan kasar a farkon wannan shekarar biyo bayan zanga-zangar da akayi na nuna kin jinin gwamnatinkasar a yankin da ake anfani da harshen turanci.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG