Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Limamin Darikar Katholika A Mali Zai Sami Karin Girma.


Papa Roma Francis
Papa Roma Francis

Fadar Papa Roman ta Vatican tace za a nada wani babban limamin cocin daga kasar Mali a matsayin daya daga cikin dattijan fadar paparoma a birnin Roma yau Laraba, duk da abun fallasar wasu kudade dake wuyarsa.

Akwai jita jitan da aka yayata a kasar Mali da Roma cewar Papa Roman Francis ba zai karawa Archbishop Jean Zerbo mukami ba, saboda wasu batutuwar da suka shafi sha’anin kudi a cocinsa a Mali. Amma jami’ai a fadar paparoma sun tabbatar a jiya Talata cewar Zerbo zai halarci bukin nada shi a a yau Laraba tare da wasu mutane hudu daga wasu kasashen.

Rahotanni sun ce Zerbo da wasu jami’an cocin Mali sun ajiye sama da dala miliyon 13 a bankin Switzerland.

Yatinda ajiye kudi a wani bankin kasar waje ba sabawa doka bane, to amma ba a tantance inda wadannan kudade suka fito ba.

Wani limamin cocin kasar Mali ya fadawa kamfanin dilancin labrun Associates Press cewar Zerbo da wasu manyan jagabanin cocin basu aikata wani mugun aiki ba, to amma kuma bai bada wani karin bayani ba.

Archbishop Zerbo ya taimaka wajen shiga tsakani a tattauna yarjejeniyar zaman lafiya ta 2015 tsakanin gwamnatin Mali da yan tawayen Abzinawa.

Yana daya daga cikin manyan lilamen addinin Krista a kasar Mali, inda Musulmi ke da matukar rinjaye.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG