Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISWAP Tana Kokarin Kafa Daula A Jihar Neja


A yayinda mayakan kungiyar boko haram ke cigaba da mamaye sassa daban daban a yankin Shiroro ta Jihar Neja dake arewa maso tsakiyar Nigeria, yanzu haka kuma gwamnatin jihar Nejan tace mayakan kungiyar Islama ta yammacin Afrika wato ISWAP na can ta fara aikin kafa wata daula a yankin Borgu.

Yankin dai na cikin gandun dajin nan na Kayinji wanda ke iyaka da Nigeria da kuma kasar jamhriyar Benin.

A wani taron manema labarai sakataren gwamnatin jihar Nejan Alh. Ahmed Ibrahim Matane yace mayakan na ISWAP sun share sama da wata guda yanzu suna aikin kafa wannan daula a wannan yanki.

Tuni dai masu sharhi da masana harkokin tsaro suka ce lamarin yana da matukar tayar da hankali. A saboda haka akwai matukar bukatar daukar mataki mai karfin gaske.

A baya dai tsohon gwamnan Jihar Nejan Dr. Muazu Babangida Aliyu ya taba fatattakar wasu masu ikirarin jihadi da suka kafa wani gari mai suna Darul Islam a yankin Mokwa dake kusa da wannan wuri Al’amari.

Babu shakka dai a yanzu hankalin jama’a ya karkata akan wannan al’amari domin ganin irin matakin da hukumomi zasu dauka.

Saurare cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG