A cikin makon jiya ne dai aka bada labarin cewa wasu mutane sanye da kayan yan banga sun auka a garin Adogon Malam ta yankin Karamar Hukumar Mashegu har sun kashe sarkin garin mai suna Malam Sa’idu Abubakar, dama wasu fulanin masu tarin yawa.
Gwamnan Jihar Nejan Alh. Abubakar Sani Bello ya ce wannan kwamiti ya kunshi kwararru akan sha’anin tsaro da shari’a kuma zai share wata guda yana gudanar da aikin binciken.
Tunda farko dai kungiyar makiyaya ta Miyatti a Nigeria ce ta bukaci gwamnatin jihar Nejan da ta gudanar da bincike akan wannan al’amari bisa la’akari da yadda abun yayi munin gaske a cewar Mataimakin Shugaban Kungiyar Miyatti Allah a Nigeria Alh. Husaini Yusuf Bosso.
Tun bayan da wasu yan bindiga suka hallaka mutane 18 a lokacin da suke sallar asuba a garin Mazakuka ne dai a farkon makon jiya wannan matsala ta kisan jama’a a yankin ta kara ta’azzara.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: