Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Na Kara Samun Karfi A Jihar Neja Mai Iyaka Da Abuja


Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja).
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja).

Kungiyar Boko Haram ta kwace kauyuka da dama a jihar Neja dake arewa maso tsakiyar Najeriya, suna baiwa mutanen kauyukan kudin suna saka su yaki da gwamnati, a cewar wani jami’in karamar hukuma da hukumar yada labaran jihar, suna fadawa Reuters

Kungiyar mai ikirarin yakin Musulunci tafi maida hankali a arewa maso gabashin kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika kana yanzu tana cikin jihar Neja wadda keda iyaka da birnin tarayya, lamarin dake tabbatar da yaduwar kungiyar a daidai lokacin da sojojin kasar ke cewa yakin da suke yi da ‘yan ta’addan na samun nasara.

Suleiman Chukuba, shine shugaban karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja mai iyaka da birnin Abuja, ya ce mayakan Boko Haram yanzu tana cikin akalla yankuna 8 a cikin 25.

“Karamar hukumar Shiroro nada mayakan kungiyar Boko Haram da basu da adadi,” inji Chukuba.

Kwamishinan yada labarai a jihar Neja Muhammad Sani Idris ya tabbatar da akwai mayakan Boko Haram wanda a farko ake musu kallon ‘yan fashi ne, wadanda tuni suke cikin jihar. Amma Idris ya ce gwamnatin jihar da jami’an tsaro sun yi kokarin dakile yaduwar su.

“Muna iya bakin kokarin mu a matsayin mu na jihar,” inji shi. “Kana zamu yi tsarin hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaron mu da ‘yan sa kai na yankuna.”

Ma’aikatar sojan kasar ta ce a watan da ya gabata kusan mayakan Boko Haram 6,000 suka ajiye makaman su, lamarin da ake dangatawa da kokarin sojojin ke yi a yaki da ‘yan ta’addan.

XS
SM
MD
LG