Shi dai mutumin ya zamana ne ‘mai ba da shawara ta sihiri ga gungun masu garkuwa da mutane a tsakanin jihar Neja da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
A bisa rahoton leken asiri, jami’an jihar da ke da alaka da rundunar ‘yan sandan sun kuma dakile shirin yin garkuwa da wasu masu ibada a wata Coci da ke kauyen Buku a karamar hukumar Abaji a babban birnin tarayya Abuja kamar yadda wadansu majiyu a Najeriya su ka bayyana.
Wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO), DSP Wasiu A Abiodun, a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar, ta ce wanda ake zargin a lokacin da ake yi masa tambayoyi ya amsa cewa shi ne jagoran ayyukan sihiri ga wasu mashahuran ‘yan bindiga da ke addabar jihohin arewa ta tsakiya; Niger, Birnin Tarayyar Abuja da jihar Nasarawa.
Yadda Aka Kama Wasu Matasa Da Ake Zargi Da Ayyukan Bata-Gari A Birnin Maidugurin Najeriya