Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Na Kara Kaimi Wajen Kai Sabbin Hare-hare A Arewacin Najeriya 

‘Yan Bindiga Na Kara Kaimi Wajen Kai Sabbin Hare-hare A Arewacin Najeriya
‘Yan Bindiga Na Kara Kaimi Wajen Kai Sabbin Hare-hare A Arewacin Najeriya

Yayin da mahukunta a Najeriya ke kokarin yakar ‘yan ta'adda, su kuwa ‘yan ta'addan sai kara samun kwarin gwiwa suke yi na kara kai sabbin hare-hare.

SOKOTO, NIGERIA - Irin hakan ne ya faru a Jihar Sakkwato dake Arewa maso Yammacin Najeriya inda kwana uku bayan da mayakan kasar suka hallaka ‘yan bindiga, suka sake daura damara da sake kai hari a yankin da ma wasu yankuna.

Duk da asarar da ‘yan bindiga ke samu ta rashin mayakansu, bai rage musu kwarin gwiwa na sake kai hare-hare, domin bayan da suka sha da kyar a garin Rabah na jihar Sakkwato, a arewa maso yammacin Najeriya sai ga shi suna kai hari a wasu garuruwa kamar wanda suka kai garin Kalmalo dake Karamar Hukumar Illela Wanda ke Kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar.

‘Yan Bindiga Na Kara Kaimi Wajen Kai Sabbin Hare-hare A Arewacin Najeriya
‘Yan Bindiga Na Kara Kaimi Wajen Kai Sabbin Hare-hare A Arewacin Najeriya

Dan majalisar jiha mai wakiltar yankin Bello Isa Ambarura ya ce ko kafin wannan harin na Kalmalo inda suka kashe mutum takwas an dauki tsawon kwanaki ana fuskantar hare-haren a karamar hukumar duk da tarin jami'an tsaro da ke aiki a yankin.

Harwayau ‘yan bindigar sun afka wa garin Rara na karamar hukumar Rabah, jiya Laraba ana tsaka da cin kasuwa suka tarwatsa jama'a suka yi abinda suke so.

Tsohon kansilan mazabar ta Rara, honorabul Danladi Rara, wanda ya shedi yadda abin ya faru, ya ce barayin sun shiga kasuwar suka rika harbe harbe suka tarwatsa jama'a suka sace dabbobi kuma suka kona ababen hawa masu yawa.

‘Yan Bindiga Na Kara Kaimi Wajen Kai Sabbin Hare-hare A Arewacin Najeriya
‘Yan Bindiga Na Kara Kaimi Wajen Kai Sabbin Hare-hare A Arewacin Najeriya

Dan majalisar jiha mai wakiltar yankin Abdullahi Zakari Rabah ya tabbatar da aukuwar harin; sai dai ya ce nan take aka dauki matakin dakile harin.

Tsohon kansilan yankin ya tabbatar da zancen dan majalisar inda ya ce sojoji sun je bayan barayin sun fice amma dai sun ga jiragen yaki biyu sun bi sawon barayin.

Mahukunta a jihar dai na ci gaba da jaddada azamar su ta ganin an samu saukin matsalar kamar yadda kwamishinan tsaro na cikin gida Abubakar Maikudi Ahmad ya bayar da tabbaci.

Yanzu dai fatan ‘yan Najeriya bai wuce a kawo karshen wannan matsala ta yadda komai zai gudana salun alun.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

‘Yan Bindiga Na Kara Kaimi Wajen Kai Sabbin Hare-hare A Arewacin Najeriya .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

XS
SM
MD
LG