Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Na Ci Gaba Da Kai Hari A Sassan Jihohin Sokoto Da Kebbi Gabanin Babban Zabe


'Yan bindiga a yankin jihar Kebbi
'Yan bindiga a yankin jihar Kebbi

Yayin da ake kusantar zabukan gama gari a Najeriya ‘yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a sassan kasar tare da kashe mutane da tarwatsa garuruwa.

Rashin tsaron na ci gaba da tayar da hankalin ‘yan Najeriya a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zabe a wannan shekarar.

Wannan ya sa jama'a ci gaba da kokawa ganin yadda matsalar ta gagari a magance ta duk da yake mahukunta na cewa suna kokarin samar da mafita.

Jihohin arewa maso yammacin Najeriya ne suka fi fuskantar wannan matsalar, kamar a jihar Sokoto ‘yan bindiga sun yi wa wani babban malamin addini kisan gilla tare da tarwatsa garuruwa da dama.

A ranar Laraba an kashe wasu mutane hudu da kuma wani babban malamin addinin musulunci, sannan aka sace mutane goma sha takwas, kamar yadda Habibu Halilu Modaci, dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Isa, ya bayyana a hirar shi da Muryar Amurka, yace sun yi ta kai koke akan wannan matsalar amma har yanzu basu ga wani sauyi ba.

Ya kuma ce a cikin makon ‘yan bindiga sun tarwatsa garuruwa hudu kuma idan abin ya ci gaba har lokacin zabe ba lallai a yi zaben kirki ba a yankunan.

Wani abu da ke daure kai game da lamarin shi ne yadda koken jama'ar da abin ke shafa ke ci gaba da zama ihunka-banza.

Shugaban Rundunar Adalci a Najeriya Bashir Altine Guyawa, yace kullum sai an kai hari a garuruwan da ke gabashin Sokoto, a yanzu duk jama'ar garuruwan sun tarwatse. Ya kuma yi fatan jami'an soja da suka shiga yankin su taka rawar gani wajen samar da sauki ga matsalolin.

A jihar Kebbi ma batun daya ne, musamman a kudancin jihar. Wani mazaunin yankin Sakaba ya ce kusan garuruwa goma sha biyar suka watse, kuma a duk rana jama'a na kauracewa garuruwansu domin su tsira.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta Kebbi ta fitar da wani bayani mai dauke da sa hannun kakakinta SP Nafi'u Abubakar da ke nuna cewa a wannan makon kwamishinan ‘yan sanda ya ziyarci yankin a kokarin auna yanayin tsaro da kuma kara daukar matakan inganta shi.

Kokarin jin ta bakin hukumomin tsaro a jihar Sokoto ya ci tura, amma rundunar ‘yan sandan jihar a ta bakin kwamishina Muhammad Usaini Gumel, ta yi ta bayar da tabbacin kudurinta na karfafa samar da tsaro a duk fadin jihar.

Yanzu dai jama'a na ci gaba da zama cikin zullumi tare da zura ido su ga abinda mahukunta za su yi yayin da ake shirin zabe.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG