Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Edo: An Kubutar Da Karin Mutum Daya Daga Fasinjojin Da Aka Sace


Jirgin kasan Najeriya
Jirgin kasan Najeriya

Hakan na nufin adadin mutanen da aka kubutar ya zuwa ranar Talata ya kai shida.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta ce an kubutar da karin mutum guda daga cikin fasinjojin da aka sace a tashar jirgin kasa a makon da ya gabata a jihar.

A ranar Asabar wasu mahara suka far wa tashar jirgin kasa ta Igueben a jihar ta Edo da ke kudu maso kudancin kasar.

Hakan na nufin adadin mutanen da aka kubutar ya zuwa ranar Talata ya kai shida.

Rahotanni sun yi nuni da cewa an yi garkuwa da mutum sama da 30.

Rundunar ‘yan sanda jihar ta ce tana kan bibiyar sahun ‘yan bindigar domin kubutar da sauran mutanen da suka rage.

Mutanen da aka sace fasinjojin ne da ke jiran jirgi don zuwa birnin Warri na jihar Delta daga karamar hukumar Igueben a jihar ta Edo.

Wannan lamari ya faru ne kusan shekara guda bayan da ‘yan bindiga suka kai hari kan wani jirgin fasinja da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja a watan Maris din bara.

Maharan sun kashe akalla mutum tara suka kuma yi garkuwa da wasu gommai.

Ko da yake, an sako dukkan mutanen a lokuta daban-daban a bara, bayan da suka kwashe watannin a hannun ‘yan bindigar.

XS
SM
MD
LG