Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Sauke Buratai, Sadique Da Karin Wasu Biyu


Hafsan Sojin Saman Najeriya Sadique Abubakar tare da Shugaba Muhammadu Buhari.
Hafsan Sojin Saman Najeriya Sadique Abubakar tare da Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban Najeriya Muhammadu Muhammadu Buhari ya maye gurbin manyan hafsoshin sojin kasar da suka yi murabus.

A ranar Talatan nan ne shugaban Najeriyar ya amince da murabus din manyan hafsoshin sojin da suka hada da babban hafsan tsaro na kasa, Janar Abayomi Olonisakin da babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas da kuma babban hafsan sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar.

Sabbin manyan hafsoshin sojin su ne Manjo Janar Leo Irabor a matsayin babban hafsan tsaro na kasa, da Manjo Janar I. Attahiru a matsayin babban hafsan sojin kasa. Sai kuma Rear Admiral A.Z Gambo a matsayin babban hafsan sojin ruwa, da kuma Air-Vice Marshal I.O Amao a matsayin babban hafsan sojin sama.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina ya fitar, shugaban Najeriyar ya gode wa tsofaffin manyan hafsoshin sojin bisa abin da ya kira “babbar nasarar da suka samu wajen tabbatar da zaman lafiya a Najeriya”, sannan ya yi mu su fatan samun nasara a rayuwarsu a gaba.

Shugaba Buhari ya kuma taya sabbin manyan hafsoshin sojin murna bisa mukamin da suka samu yanzu, sannan ya hore su da su kasance masu biyayya da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukansu.

In za a tuna dai, mutane da dama a Najeriyar sun yi ta yin kira ga shugaban kasar da ya canja manyan hafsoshin tsaron, ganin yadda matsalar tsaro a kasar ke ci gaba da tabarbarewa.

Sai dai a baya shugaba Buhari bai saurari kiraye-kirayen sauke manyan hafsoshin ba, abin da ya sa masu sharhi kan sha’anin tsaro ke nuna shakku a ikirarin gwamnatin kasar na yaki da ‘yan bindiga musanman mayakan Boko Haram.

Abin jira a gani yanzu shi ne, ko wadannan sabbin manyan hafsoshin soji da aka nada za su kawo babban canji da mutane suka dade su na jira na kawo karshen matsalolin tsaro da kasar ke fama su.

XS
SM
MD
LG