Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Dillalin Muggan Makamai A Jihar Katsina


Rundunar 'yan sandar jihar Katsina ta kama wani dillalin manyan makamai, da wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne.

Rundunar 'yan sanda ta Jihar Katsina dake Arewacin kasar ta samu nasarar kama wani mai safar muggan makamai, tare da mutane 17 da ake zargin 'yan ta'adda ne a gidan sa.

A lokacin wani samame da aka kai gidan shi Mal. Haruna, an samu wasu mutane 15, wadanda dukkan su mutanen jamhuriyar Nijar ne. An samu makamai a gidan, wanda aka tabbatar da cewar yana dillancin su ne.

Kwamishinan 'yan sandar jihar ta Katsina CP Sanusi Buba ne dai ya bayyanar da wannan nasarar da suka samu, jim kadan bayan ganawarsa da manema labarai.

A cewar kakakin rundunar 'yan sanda a jihar SP Gambo Isah, sun samu harshashin manyan bidiga guda 179, a hannun Haruna wanda ke zaune a kauyen Saureya, da ke karamar hukumar Kaita, kana an same shi da bindigar nan da ake kira Mashingon guda 2, bindiga ce da sojoji kadai ke mallakar irinta a Najeriya.

Gara rahoton wakilinmu Sani Shuaibu Malumfashi a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG