Shugaban Kungiyar Malaman Makarnatun Firamare a Jihar Borno, Comrade Bulama Abiso, shi ne ya bayyana hakan a wajen bukin ranar tunawa da malamai ta duniya da aka gudanar a garin Maiduguri.
Ya roki gwamnatin jihar Borno da hukumomin tsaro da su tabbatar da daukar karin matakan kare malamai, wadanda suke sadaukar da rayukansu domin koyar da dalibai a jihar.
haka kuma, Comrade Bulama Abiso, ya roki gwamnati da ta duba batun albashi mafi kankanci da ya kamata a rika biyan malamai, yana mai fadin cewa a hukumance, su na goyon bayan matakin tacewa da tabbatar da malaman makarantun da gwamnati take aiwatarwa.
Wakilin Sashen Hausa, Haruna Dauda Biu, ya aiko da cikakken bayanin wannan buki a bayan ya tattauna da shugaban kungiyar malaman.