Firai Ministan kasar Birji Rrafini ne ya bukaci sanin mizanin adadin yan majalisun kasar da ke goyon bayan gwamnatinsa yan makwanni bayan kulla wani sabon kawancen da jam’iyyun adawar kasar suka yi cikinsu harda jam’iyyar shugaban majalisar.
Wakilinmu dake Niamey Abdoulaye Mamane Amadou ya ruwaito cewa, ayar doka mai lamba dari da bakwai zuwa dari da takwas ta kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar ce ta ba gwamnati na wannan hurumi na aika wata ayar doka gaban majalisar dokoki a matsayin kalubalai wajen auna nauyin da take da shi gaban majalisar saboda samun yardarta a kai. Wanda idan haka bata samu ba Firai minista a sauran membobinsa zasu mika murabus ga shugaban kasa.
An shafe wunin jiya ana muhawara a zauren majalisa a kan wannan batun da wani dan majalisa ya gabatar abinda ya kai ga kada kuri’a da ‘yan majalisa 70 suka nuna goyon bayansu ga shirin a yayinda ‘yan majalisa arbain da uku suka kada kuri’ar rashin yardarsu da ma kin yarda da gwamnatin baki daya da Firai Minista Birji Rafini yake jagoranta.
Firai ministan ya bayyana wannan goyon bayan da gwamnatin ta samu a matsayin nasarar jamhuriyar Nijar baki daya.
Wadansu ‘yan jam’iyar hamayya dai sun yi zargin cewa, an bada kudi ne domin neman goyon bayan ‘yan majalisa.