A bayan ganawar da suka yi a fadar shugaban kasa, Mr. Ban da shugaba Issoufou tare da sauran jami'ai sun zarce zuwa majalisar dokoki ta kasa a inda suka gudanar da taron 'yan jarida na hadin guiwa.
Babban sakataren MDD, yace yankin Sahel ya shiga idanun duniya a bayan abubuwan da suka wakana a kasar Mali, kuma a yanzu duniya ta san cewa yankin yana fama da matsaloli na tsaro, makamashi, noma, kiwo da sauransu. Don haka ne majalisar, tare da hadin kan babban bankin duniya, da bankin raya kasashen Afirka, da Majalisar tarayyar Turai suka hadu domin kirkiro da shirin tallafawa yankin na tsawon shekaru 7.
A Jamhuriyar Nijar kawai ma, cibiyoyin zasu bayar da tallafin Euro miliyan 181 domin gudanar da wadannan ayyukan, wadanda kuma sun hada har da samar da wadataccen abinci da ruwan sha.
Shugaba Mahamadou Issoufou yace wannan tsari na MDD ya dace da irin shirye-shiryen shugabannin yankin na Sahel, kuma zai tallafa ma yunkurin shugabanni da al'ummar yankin na wanzar da tsaro da kawar da talauci.
Daga bisani, babban sakataren na MDd, Ban Ki-moon, ya gabatar da jawabi mai ratsa jiki a gaban majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar.
Tuni tawagar ta wuce zuwa kasar Burkina Faso.
Ga Abdoulaye Mamane Ahmadou da karin bayani.