Jam’iyyar Lumana Africa ta fice daga cikin gwamnatin gamin-gambiza ta Junhuriyar Nijer, ta kuma umurci duk ministocinta da su ajiye mukamansu
WASHINGTON, DC —
Jam’iyyar Lumana Afrika ta tsohon frayim-ministan Junhuriyar Nijer Hamma Amadou yau ta fice daga gwamnatin gamin-gambiza ta shugaba Mouhammadou Issouffou. Manyan kusoshin Lumana din sun yi zarge-zarge da dama na dalilansu na ficewa daga kawancensu da jam’iyyar PNDS Tarayya. Daga birnin Niamey, ga rahoton da Abdoulaye Mamane Amadou ya aiko mana kan wannan sabon lamari: