An yi taron ministocin ne ranar talatin ga watan jiya inda ofishin ministan cikin gida ya sanarda tsige magajin garin kuma shugaban majalisar mashawartan birnin garin Umaru Mummuni Dogari. Gwamnati tana zargin shi ne da yin ba dai-dai ba da dukiyar gwamnati ta hanayar jinginar da wasu kadarori mallakar kasa ga wani banki domin samun lamuni ba tare da neman shawara ba daga gwamnati da kansiloli kananan hukumomin da suke cikin gwamnatin birnin.
Kakakin majalisar zartaswar kasar kuma ministan sharia ya kirawo taron manema labarai domin bada karin haske bisa ga hukumcin tsige magajin garin da majalisar ta dauka. Ya ce ranar Alhamis aka kawo mashi takardun kadarorin da magajin garin ya bayar jingina har da gidan da yake zaune ciki. Ya ce doka bata bashi izinin yin haka ba. Ba'a yadda a yi jingina da kayan gwamnati ba domin a karbi lamuni a yiwa gwamnati aiki. Doka ta ce duk wanda ya yi hakan dole a tsige shi.
Dama 'yan majalisar kasar sun nemi a tsige magajin garin kuma zasu jefa kuri'ar amincewa ko rashin amincewa da bukatar ranar Alhamis. To amma sai gashi gwamnati ta yi gaban kanta ta yiwa majalisar dokoki katsa landan lamarin da wasu 'yan majalisar suke cewa tsigeshi tamkar bita da kuli ne kawai.
Ga rahoron Abdullahi Mamman Ahmadu.