Kungiyoyi biyu ne suka bullo a cikin ‘yan kwanakin nan da nufin kalubalantar gwamnatin PNDS Tarayya a kan abin da suka kira rashin sanin makaman mulki. Wata kungiya karkashin MPN-Kishin Kasa, ta sanar da shirinta a karshen mako na fafatawa da gwamnati saboda rashin bai wa bukatun talaka muhimmanci.
Da take mayar da martani ta bakin kakaninta Asoumana Mahamadou, jam’iyyar PNDS mai mulki ta ce, wadanda ke shirya irin wadannan kawance domin su fafata da gwamnatin ai daga gwamnatin ne aka kore su, kuma kowa na sane da dalilin da yasa aka kore shi ko kuma ya bar gwamnati.
Su ko manyan jam’iyyun adawar kasar sun yi na’am da matakan da tsofaffin jami'an gwamnati suke dauka na kalubalantar gwamnati.
Alhaji Doudou Mahamadou kusa ne a jam’iyun adawa kasar, ya ce ganin yanda wadannan kungiyoyi suka bar mulki suka koma adawa, hakan na tabbatar da cewa su 'yan adawa na kan gaskiya, ya kuma yi marhabi lale da kungiyoyin kawancen.
PNDS mai mulki ta ce wannan yunkuri da ‘yan adawa ke yi ba zai kai su ga cin gaci ba, saboda sun rufe idanuwansu a kan ayyukan ci gaba da shugaban kasa ke yi a cikin kasar.
Kakakin jam’iyar PNDS ya ce sun yi adawa mai tsafta a can baya lokacin mulkin Tandja Mamadou, suka ba shi dama ya yi mulki suka kuma sun nuna ayyuka masu kyau da maras kyau da ya yi, amma sai yanzu ake samun akasin haka, saboda kwadayin mulki, komai gwamnati ta yi mutane ba su gani.
Wakilin muryar Amurka a birnin Yamai, Sule Mumuni Barma na da karin bayani a cikin wannan rohoton.
Facebook Forum