Sarkin kabilar Yarbawa na jihar Borno Alhaji Hassan Alao Yusuf ya kira wani taron bude baki a fadarsa dake Birnin Maiduguri inda ya gayyato kabilu daban daban da mabiya addinai daban daban tare da ‘yan asalin jihar.
Sarkin, Alhaji Alao Yusuf ya ce matakin da shugaba Buhari ya dauka na karama marigayi Cif MKO Abiola “mataki ne mai kyau. Mataki ne da ya kamata an dauka tun da dadewa amma shugabannnin baya sun ki yinshi.
Akan adawa da wasu su keyi da matakin da shugaban Najeriya ya dauka, sarkin Yarbawan y ace a duniya komi mutum ya yi za’a samu masu adawa dashi, saboda haka baa bun mamaki ba ne. A cewarsa suna goyon bayan abun da shugaban kasa ya yi.
Dangane da dalilinsa na kiran taron shan ruwa da kabilu daban daban da duk mabiya addinai yace ya yi hakan ne domin karfafa dankon zumunci tsakaninsu da sauran mutane da ma ‘yan asalin jihar da suke ciki.
Dr Bulama sakataren dattawan jihar Borno wanda ya kasance wurin shan ruwan y ace sarkin Yarbawan ya kira kowace kabila dake zaune a Borno kuma duk shugabanninsu sun amshi goron gayyatarsa. An zauna tare dasu sun yi sallah tare sun kuma sha ruwa tare. A cewarsa abun da aNajeriya take bukata ke nan. Y ace zasu je gida su gayawa ‘ya’yansu da jikokinsu cewa ga yadda ya kamata su zauna da juna.
Dan majalisar dokokin jihar Borno Abubakar Tijjani y ace abun da sarkin Yarbawan jihar Borno ya yi, misali ya koya masu saboda ya gayyato mutane ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba. Babu kabilar da bata kasance a wurin ba.
Shi ma tsohon shugaban kungiyar kabilun Igbo da ya kasance a wurin shan ruwan y ace dukansu kabilu daban daban sun zauna tare sun yi bude baki. A cewarsa abun yabawa ne saboda irin wannan taron zai kawo zaman lafiya.
A saurari rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Facebook Forum