Rundunar ‘yan sandan jihar Texas ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon wani harin harbin kan mai uwa da wabi a yammacin jihar ta Texas jiya Asabar ya kai mutane 7, akalla mutane 20 kuma sun jikkata.
Shugaban ‘yan sandan garin Odessa Michael Jerke ya kira ranar jiya “mai muni” bayan mace-macen da aka samu sakamakon harbi a Odessa da kuma Midland dake kusa duk a jihar ta Texas.
‘Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da mutumin da ake zargi da kai harin ya kwace wata motar kai sakonni ta hukumar UPS, daga nan ya fara zagayawa da motar yana harbin jama’a.
Maharin, wanda aka bayyana cewa bature ne mai kimanin shekaru 30 da haihuwa, an harbe shi har lahira bayan da wani dan sanda ya datse shi a wani wurin ajiye motoci na wani gidan silima, a cewar hukumomi. Sai dai basu bayyana dalilin kai wannan harin ba wanda har da ‘yan sanda 3 cikin wadanda suka jikkata.
Mr. Jerke ya ki ya bayyana sunan dan bindigar. Haka kuma hukumar ‘yan sandan ba ta fitar da sanarwa akan shekarun wadanda harin ya shafa ba da kuma halin da suke ciki.
Facebook Forum