Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Lallai Akwai Yiwuwar Zai Gana Da Shugaban Iran


Shugaba Trump da Hassan-Rouhani
Shugaba Trump da Hassan-Rouhani

Shugaban Iran Hassan Rouhani, ya ce idan har takwaran aikinsa na Amurka Donald Trump na so su gana, to ya fara sharar fage da dage takunkuman da ya kakaba wa Iran.

A cewar Rouhani, Iran ta riga ta bayyana cewa, ba makamin nukiliya take shirin kerawa ba, yana mai cewa takunkuman da aka saka musu, “haramtattu ne kuma rashin adalci ne,”

Yace ko a baya-bayan nan, shi da kansa Shugaba Trump ya bayyana yadda takunkuman suke tasiri akan kasar ta Iran.

Shugaba Trump ya ce, lallai takunkuman na cutar da su, ba na son ganin hakan, ba zai yi wu mu bar su su mallaki makamin nukiliya ba, ba zai yi wu ba, lallai akwai yiwuwar za mu gana.

Shugaban Faransa Eammanuel Macron ne dai, ya yi ta fadi-tashin ganin ya sasanta Amurkan da Iran kan wannan takaddama.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG