Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnoni Sun Amince Da Dubu 22, 500 a Matsayin Albashi Mafi Karanci


Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdul'aziz Abubakar Yari na Jihar Zamfara
Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdul'aziz Abubakar Yari na Jihar Zamfara

Sai dai hadakar kungiyoyin kwadagon kasar ta NLC ta yi watsi da wannan sabon tayi da Gwamnoni suka yi, inda suka ce suna kan bakarsu ta cewa sai an biya 30,000.00.

Gwamnonin Najeriya sun amince za su biya Naira dubu 22, 500 a matsayin albashi mafi karanci wanda hakan ya gaza Naira dubu 30 da kungiyoyin kwadago suka nema.

Kungiyar gwamnonin sun cimma wannan matsayar ce bayan wani taro da suka yi a jiya Litinin.

Shugaban kungiyar gwamnonin na Najeriya, Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya fadaw amanema labarai cewa sun yi la’akkari da cewa akwai bukatar kada albashin ma’aikata kada ya wuce kashi 50 cikin 100 na kudaden shigar kowacce jiha.

Sai dai hadakar kungiyoyin kwadagon kasar ta NLC ta yi watsi da wannan sabon tayi da Gwamnoni suka yi, inda suka ce suna kan bakarsu ta cewa sai an biya dubu 30.

A wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust, Shugaban kungiyar ta NLC, Ayuba Wabba, ya ce abin da za su mutunta kawai shi ne matsayar da aka cimma tsakanin bangarori uku, wato gwamnatin tarayya da gwamnoni da kungyar ta kwadago, inda ya yi ikrarin cewa dukkanin bangarorin uku sun amince akan dubu 30.

A baya gwamnatin tarayya ta nemi da za ta biya dubu 24 kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A makon da ya gabata, kungiyar ta kwadago ta ce ta lura gwamnati na mata wasa da hankalin wajen aiwatar da matsayar da aka cimma ta dubu 30.

Hakan ya sa ta ba da umurni ga ma’aikatan kasar da su shiga yajin aiki nan da ranar 6 ga watan Nuwamba idan har ba a aiwatar ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG