Kungiyar kwadago a karkashin shugabancin Comrade Ayuba Waba, ba za ta sake zama da wani ko a yi wata yarjejeniya ba tun da an riga an tattauna da gwamnati an amince cewa albashi mafi kankanta ya zama Naira 30,000.00, inji Sakataren tsare-tsaren kungiyar kwadago ta Najeriya, Comrade Nuhu Toro.
Toro ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Muryar Amurka, inda ya yi zargin cewa gwamnati na nuna mata fuska biyu.
“Dubu 30 din nan ba abin da kungiyar kwadago ta so ma’aikacin Najeriya ya amsa ba ne, muka yi hakuri…. Amma mun lura cewa dubu 30 din ma tana tafiyar hawainiya.” Toro ya kara da cewa.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce kungiyar ta kwadago ba ta yi mata adalci ba idan ta ce tana kwan-gaba kwan-baya kan batun albashin, a cewar Ministan Kwadagon Najeriya, Chris Ngige.
“Duk wanda ya ce muna kwan-gaba kwan-baya kan batun, bai yi mana adalci ba, domin muna yin abin da ya kamata ne, muna da kishin ma’aikata, sannan ba mu sallami kowa daga aiki ba kuma ba mu saka takunkumi kan karin girma ga ma’aikata ba.” Ngige ya ce.
Amma kungiyar ta kwadago ta ce idan har daga nan zuwa watan 11 ma’aikacin Najeriya bai samu karin albashi ba, za ta tsunduma cikin yajin aikin na gama-gari.
Kungiyar ta kara da cewa kada ma’aikata su zabi gwamnatin da ta ki kara masu albashi mafi kankanta na Naira 30,000.00.
“Jihar da gwamna ya ce ba zai iya biyan albashi mafi kankanta 30,000.00 ba kada su zabe shi a 2019 idan zabe ya zo.” Inji Toro.
A jima ana ta da jijiywar wuya tsakanin bangarorin biyu kan albashi mafi karanci.
Ana biyan ma'aikaci karancin albashi Naira 18,000.00 amma kungiyar na so a kai shi zuwa Naira 30,000.00.
Facebook Forum