Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Zaben Shugaban Kasar Chadi Ke Gudana


Presidential election in N’djamena
Presidential election in N’djamena

A ranar litinin ake kammala zaben shugaban kasar Chadi inda fararen hula suka fita rumfunan zabe, kwana daya bayan da sojoji suka kada kuri’unsu. Shugaban rikon kwarya Janar Mahamat Idriss Deby dai na fuskantar kalubale guda tara da suka hada da firaministan sa na yanzu.

Zaben wanda aka tsara shi domin kawo karshen mulkin soja na tsawon shekaru uku, ya zuwa yanzu ana gudanar da shi cikin lumana. Sai dai ana zaman dar-dar game da hana daukar hotunan sakamakon zabe a rumfunan zabe.

Daruruwan mutane ne suka fara isa rumfunan zabe a N'djamena babban birnin kasar Chadi da misalin karfe 5:30 na safe agogon kasar.

Daga cikin masu kada kuri'a a jami'ar N'djamena har da dalibi Abdel Koura mai shekaru 29 da haihuwa. Ya ce ya fito da wuri domin kada kuri’a saboda yana son shugaban kasa da zai kawo zaman lafiya da samar da ayyukan yi ga matasan da ba su da aikin yi bayan sun kammala karatunsu.

Koura ya ce zabe hakkinsa ne da tsarin mulki ya bashi. Ya ce yana kira ga daukacin fararen hula musamman matasa da su fito da yawan gaske domin zaben shugabansu cikin kwanciyar hankali. Ya ce yana kuma rokon gwamnatin rikon kwarya ta kasar Chadi da ta kaucewa hargitsi ta hanyar tabbatar da cewa zaben ya gudana cikin gaskiya da adalci kuma wanda zai yi nasara shi ne wanda farar hula suka zaba.

An gudanar da zaben wuri lami lafiya. Sai dai hukumar gudanar da zabe ta kasar Chadi, wadda aka fi sani da ANGE, ta ce dubban rumfunan zabe sun bude a makare saboda abin da suka kira matsalar kayan aiki.

Shugaban rikon kwarya na kasar Chadi, Janar Mahamat Idriss Deby ya kada kuri'a a gunduma ta biyu ta N'djamena, ya kuma roki fararen hula da su fito baki daya su gudanar da aikin da ya rataya wuyansu na zaben mutumin da zai tafiyar da al'amuran Chadi na tsawon shekaru biyar masu zuwa.

ANGE ta ce mutane miliyan 8.2 ne suka yi rijistar zabe. Ta ce an tura sojojin Chadi don kare lafiyar masu kada kuri'a a rumfunan zabe sama da 26,500.

Kasar Chadi ta ce sama da masu sa ido na kasa da kasa 2,500 daga kungiyoyi 120 ne aka amince da su sanya ido a zaben. Ta ce an yi watsi da aikace-aikacen wasu kungiyoyi 60 saboda rashin mutunta dokokin kasar.

Cyrille Nguiegang Ntchassep ita ce kakakin masu sa ido daga hukumar kula da tattalin arzikin Afirka ta tsakiya mai kasashe shida. Yana da damuwa cewa zaman lafiya ba zai tabbata ba.

Ya ce tashe-tashen hankula da ake ganin za a iya yi kan hana daukar hotunan sakamakon zabe a rumfunan zabe da buga su a shafukan sada zumunta da rediyo da talabijin na iya rikidewa zuwa rikici mai tsanani saboda fararen hula na tunanin cewa hukumar gudanar da zabukan kasar Afirka ta tsakiya na karkashin Deby ne.

Ntchassep ya ce bai fahimci dalilin da ya sa Chadi ba ta son bayyana sakamakon zabe nan da kwana guda ko biyu kamar yadda ya faru a zaben shugaban kasar Senegal da aka gudanar a ranar 24 ga Maris ba.

'Yan adawa da kungiyoyin farar hula da suka hada da babban mai adawa da jam'iyyar Transformers Party of Deby Succces Masra, sun ce sun shirya daukar hotunan sakamakon zaben da kuma rabawa ga kasashen duniya. Sun ce an dauki matakin ne don hana ANGE magudin zabe a matsayin dan takarar Deby.

Tahir Oloy Hassan shi ne kakakin ANGE. Hassan ya ce ANGE kungiya ce ta dindindin, mai zaman kanta kuma ba ta nuna son kai wacce ba ta samun umarni daga kowace hukuma ta jiha ciki har da Deby.

Ya ce hana daukar hotuna ko bidiyo na takardar sakamako da kuma haramtawa kafafen yada labarai shiga wasu rumfunan zabe da kuma wuraren da ke da muhimmanci shi ne a rage tashe-tashen hankula da ka iya tasowa daga labaran karya da kuma mutanen da ke son ganin Chadi cikin rudani.

Ya ce ikirari da 'yan takaran adawa suka yi na cewa an umurci sojojin Chadi da su zabi Deby, lokacin da suka je rumfunan zabe ranar Lahadi ba ta da tushe.

ANGE ta ce har zuwa ranar 21 ga watan Mayu ta na da damar buga sakamakon wucin gadi, kuma majalisar tsarin mulkin kasar Chadi ce kadai ke da hurumin bayyana tabbataccen sakamako.

An tsara zabukan ne domin kawo karshen shekaru uku na mika mulki bayan mutuwar Idriss Deby Itno a shekarar 2021.

'Yan adawar Chadi da kungiyoyin farar hula sun ce mulkin karamin Deby ya kasance da tashe-tashen hankula na siyasa da suka hada da zanga-zangar neman dimokradiyya a watan Oktoban 2022, inda jami'an tsaron kasar dake Afirka ta tsakiya suka kashe akalla mutane 50 tare da jikkata 300 tare da kame wasu daruruwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG