Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashim Shettima Na Halartar Taron Kasuwanci A Amurka


Kashim Shettima (Facebook/Bola Ahmed Tinubu Support Group Germany)
Kashim Shettima (Facebook/Bola Ahmed Tinubu Support Group Germany)

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya tashi daga Abuja zuwa birnin Dallas na kasar Amurka, domin wakiltar shugaba Bola Tinubu a taron kasuwanci na Amurka da Afirka na 2024 wanda kungiyar kamfanoni kan Afirka ta shirya.

WASHINGTON, D. C. - A wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce mataimakin shugaban kasar zai bi sahun sauran shugabannin siyasa da na kasuwanci a fadin Afirka a wajen taron da ke kunshe da manyan batutuwan da za a tattauna da harkokin kasuwanci da kulla kawance a fannonin cinikayya.

Daga cikin shugabannin Afirka da ake sa ran za su halarci taron akwai Shugaba Joseph Boakai na na kasar Liberia; Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera; Shugaba Joao Lourenco na Jamhuriyar Angola; Shugaba Mokgweetsi E. K. Masisi na Jamhuriyar Botswana; Shugaba José Maria Neves na Jamhuriyar Cabo Verde, da Mataimakin Firayim Minista na Masarautar Lesotho, Honourable Nthomeng Majara.

Baya ga taron kolin, ana sa ran Shettima zai yi jawabi a wani taro da zai duba batun zuba jari a fannonin ababen more rayuwa a nahiyar Afirka tare da mai da hankali kan tasiri da samun riba.

Har ila yau, an shirya Shetima Zai yi jawabi a gaban wani babban kwamiti kan harkokin noma, inda zai mayar da hankali kan sauya akalar tafiya daga "matsalar karancin hanyoyin samun abinci zuwa harkokin kasuwancin albarkatun noma da suka bunkasa"

Sanarwar ta kuma kara da cewa, mataimakin shugaban kasar zai yi jawabi a wani taro kan makomar fannin samar da wutar lantarki a nahiyar Afirka da kuma wani taro da zai halarta don tallata shirin saka hannun jari a Najeriya, baya ga wasu taruka da zai halarta.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG