Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Afkawa Wani Gari A Kaduna, Tare Da Hallaka Mutane 6


Yan bindiga
Yan bindiga

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Mansir Hassan, ne ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda yace an kama daya daga cikin maharan.

‘Yan bindiga sun hallaka mutane 6 sa’ilin da suka afkawa garin Ambe dake karamar hukumar sanga, ta jihar Kaduna, a daren jiya Lahadi.

A cewar Mansir Hassan, bayan samun kiran gaggawa jami’an ‘yan sanda daga caji ofis din Sanga da hadin gwiwar dakarun aikin wanzar da zaman lafiya na “Operation Safe Haven”, suka garzaya garin tare da yin musayar wuta tsakaninsu da ‘yan bindigar inda suka yi nasarar kama daynsu a yayin da saura suka arce cikin daji da raunukan harsashi.

A wani labarin kuma, sanarwar da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jema’a da Sanga, Daniel Amos, ya fitar tace an hallaka mutane 6 tare da jikkata wasu 8 a yayin harin, wadanda ke samun kulawa a asibiti a halin yanzu.

A yayin da yake allawadai da harin na baya-bayan nan wanda manufarsa shine tarwatsa zaman lafiya da tsaro a mazabar, dan majalisar tarayyar, ya bukaci mazauna karamar hukumar Sanga su kwantar da hankulansu tare da zaunawa lafiya a yayin da suke kokarin lalubo hanyoyin magance matsalar tsaro a yankin.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG